Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.
Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”
“Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci daga zuriyar Dawuda Wanda zai ci sarauta. Zai yi sarauta da hikima, Zai aikata abin da yake daidai a ƙasar.
Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.