Domin ya ce, “Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa, Na kuma taimake ka a ranar ceto.” Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!
to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama'ar Isra'ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.
“Ya ku 'yan'uwa, Isra'ilawa, ku ji wannan magana. Yesu Banazare, mutumin da Allah ya tabbatar muku cewa shi yardajjensa ne, ta mu'ujizai, da abubuwan al'ajabi, da alamu waɗanda ya yi ta wurinsa a cikinku, kamar yadda ku kanku kuka sani,
Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.”