33 Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”
33 za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.”
cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.”
Dā kuwa muna bege shi ne zai fanshi Isra'ila. Hakika kuma, bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abu.
suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.
Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
Gama za a bāshe shi ga al'ummai, a yi masa ba'a, a wulakanta shi, a kuma tofa masa yau.
Amma ko ɗaya ba su fahimci waɗannan abubuwa ba, domin zancen nan a ɓoye yake daga gare su, ba su ma gane abin da aka faɗa ba.