Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”
Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina.
Da Yesu ya ji haka, ya ce masa, “Har yanzu abu guda ne kawai ya rage maka, ka sayar da duk mallakarka, ka rarraba wa gajiyayyu, za ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”