Luka 18:13 - Littafi Mai Tsarki13 Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.