“Kaitonku, Farisiyawa! Ga shi, kuna fitar da zakkar na'ana'a da karkashi, da kuma kowane ganyen miya. Amma kun ƙi kula da aikata gaskiya da ƙaunar Allah. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da waɗancan ba.
“In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.
“In za ku yi addu'a, kada ku zama kamar munafukai, don sun cika son yin addu'a a tsaye a majami'u da kan hanya, wai mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun sami iyakar ladansu.
“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
Da Ubangiji ya sadu da Bal'amu, sai Bal'amu ya ce wa Ubangiji, “Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimi guda da rago guda a kan kowane bagade.”
Gama ni Ubangiji na ba su zaka da Isra'ilawa suke kawo mini ta hadaya ta ɗagawa ta zama gādonsu. Saboda haka ne, na ce ba su da gādo tare da Isra'ilawa.”