Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 18:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don yă koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 18:1
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku lazamci yin addu'a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah,


Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a.


Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.


a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.


Sa'an nan za ku yi kira a gare ni, ku yi addu'a a wurina, zan kuwa ji ku.


Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”


Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.


Kai ne Allahna, saboda haka ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, Ina yin addu'a a gare ka dukan yini.


Zai saurari jama'arsa wadda ya rabu da ita, Zai kuwa ji addu'arta.


Saboda haka, da yake muna da wannan hidima bisa ga jinƙan Allah, ba za mu karai ba.


Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.


Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da kai, ya Ubangiji. Addu'ata kuwa ta kai gare ka a Haikalinka tsattsarka.


Saboda kakan amsa addu'o'i, Dukan mutane za su zo wurinka.


Hakika zan rayu domin in ga alherin Ubangiji Da zai yi wa jama'arsa.


Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.


Ba za su bari ya huta ba, sai ya ceci Urushalima tukuna, Ya sa ta zama birnin da dukan duniya za ta yaba wa.


Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a.


Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ