35 Za a ga mata biyu suna niƙa tare, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.
35 Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.”
Za a ga mata biyu suna niƙa, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.
Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.
Filistiyawa fa suka kama shi, suka ƙwaƙule idanunsa, suka gangara da shi zuwa Gaza. Suka ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla. Ya yi ta niƙa a kurkuku.
Ina gaya muku, a wannan dare za a ga mutum biyu a gado ɗaya, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.