Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 17:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan, haka ma, Ɗan Mutum zai zama a ranar bayyanarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 17:24
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.


A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.


Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su, Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya, Ubangiji Allah zai busa ƙaho, Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.


Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa'an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.


Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, domin ranar komowar Ubangiji ta yi kusa.


kada ku yi saurin jijiguwa a zukatanku, ko kuwa hankalinku yă tashi, saboda faɗar wani ruhu, ko wani jawabi, ko wata wasiƙa a kan cewa daga gare mu suke, cewa ranar Ubangiji ta zo.


Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.


A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.


Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”


“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.


Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.


Ba a kunna fitila a rufe ta da masaki, sai dai a ɗora ta a kan maɗorinta, sa'an nan ta ba duk mutanen gida haske.


wanda zai tabbatar da ku har ya zuwa ƙarshe, ku kasance marasa abin zargi a ranar Ubangijinmu Yesu Almasihu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ