Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.
sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,
Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”
Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.