Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 17:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai ya ce wa almajiransa, “Sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadinsu!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 17:1
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin!


Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan'uwana tuntuɓe.


Saboda haka kada mu ƙara ganin laifin juna, gara mu ƙudura, don kada kowannenmu yă zama sanadin tuntuɓe ko faɗuwa ga ɗan'uwansa,


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


Ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.


Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”


Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikkilisiyar Allah,


Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal'amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra'ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.


Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.


Ibrahim ya ce masa, ‘In dai har ba su saurari littattafan Musa da na annabawa ba, ko da wani ya tashi daga cikin matattu ma, ba za su rinjayu ba.’ ”


To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ