Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 15:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 15:30
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda yake ƙaunar hikima yana faranta zuciyar mahaifinsa. Amma wanda yake abuta da karuwai zai lalatar da dukiyarsa.


Sai Bafarisiyen ya miƙe, ya yi addu'a ga kansa ya ce, ‘Ya Allah, na gode maka, da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata, ko ma kamar mai karɓar harajin nan.


Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”


Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu.


Su duk sun bayar daga yalwa tasu ne, ita kuwa daga cikin rashinta ta ba da duk abin da take da shi, duk ma da kuɗinta na abinci.”


Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina.


Sai uban ya ce masa, ‘Ya ɗana, ai, kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ