Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 15:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 15:29
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Tun da ka ce, kai mai arziki ne, cewa ka wadata ba ka bukatar kome, ba ka sani ba kuwa kai ne matsiyacin, abin yi wa kaito, matalauci, makaho, tsirara kuma.


Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”


Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar.


Dā kam, sa'ad da ban san shari'a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu.


Domin ina tsoronka, don kai mutum ne mai tsanani, son banza a gare ka, kakan girbi abin da ba kai ka shuka ba.’


Sai kuma ya ba da misalin nan ga waɗansu masu amince wa kansu, wai su masu adalci ne, har suna raina sauran mutane, ya ce,


Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da yake wajibinmu kurum.’ ”


Ina dai gaya muku, haka kuma, za a yi farin ciki a Sama, a kan mai zunubi guda da ya tuba, fiye da kan adalai tasa'in da tara waɗanda ba su bukatar tuba.”


suna cewa, ‘Na bayan nan, ai, aikin sa'a guda kawai suka yi, ka kuwa daidaita mu, mu da muka yini zubur muna shan wahala da zafin rana.’


Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.


su kuma tambayi firistocin Haikalin Ubangiji da annabawa, cewa ko ya kamata su yi baƙin ciki da azumi a watan biyar kamar yadda suka saba yi a shekarun baya?


Sa'an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.


To, ina kuma fariyarmu ta shiga? Ina kuwa! Ta wace hanya aka kawar da ita? Ta aikin lada? A'a, sai dai ta hanyar bangaskiya.


Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.


Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa.


Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ