6 Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.
6 Suka rasa abin faɗi.
Daga nan kuma ba su yi ƙarfin halin tambayarsa wani abu ba.
Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi.
Domin ni ne zan ba ku ikon hurci, da kuma hikima wadda duk abokan adawarku, ba za su iya shanyewa ko musawa ba.
Sai suka kasa kama shi a kan wannan magana gaban mutane. Saboda kuma mamakin amsarsa, suka yi shiru.
Da ya faɗi haka, sai duk abokan adawarsa suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwan al'ajabi da yake yi.
Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.