50 Ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa ɗokanta ƙwarai har a yi mini ita!
50 Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta!
Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.
Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah! Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.”
Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba.
To, ga shi kuma, yanzu zan tafi Urushalima, Ruhu yana iza ni, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba,
Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Mai da takobinka kube. Ba sai in sha ƙoƙon da Uba ya ba ni in sha ba?”
yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.
“Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru!