Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 12:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Amma zan gaya muku wanda za ku tsorata. Ku ji tsoron wannan da in ya kashe, yana da ikon jefawa a cikin Gidan Wuta. Hakika, ina gaya muku, shi za ku ji tsoro!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 12:5
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,


Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.


Sai ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi. Ku yi masa sujada, shi da ya halicci sama, da ƙasa, da teku, da kuma maɓuɓɓugan ruwa.”


Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.


Mutuwa ce maƙarar dukan mugaye, Da dukan waɗanda suke ƙin Allah.


Tsoron Ubangiji yakan ba da tabbatarwa, da zaman lafiya ga mutum da iyalinsa.


Sa'an nan aka jefa mutuwa da Hades a tafkin nan na wuta. Wannan ita ce mutuwa ta biyu, wato, tafkin wuta.


A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.


Sa'an nan zai ce wa waɗanda suke na hagun, ‘Ku rabu da ni, la'anannu, ku shiga madawwamiyar wuta, wadda aka tanadar wa Iblis da mala'ikunsa.


Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Sarkin dukan al'ummai? Ka isa a ji tsoronka, Gama babu kamarka a cikin dukan masu hikima na al'ummai, Da kuma cikin dukan mulkokinsu, Ba wani kamarka.


Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.”


don gudun Kaldiyawa, gama suna jin tsoronsu, domin Isma'ilu ɗan Netaniya ya kashe Gedaliya ɗan Ahikam wanda Sarkin Babila ya naɗa shi mai mulkin ƙasa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ