Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 12:48 - Littafi Mai Tsarki

48 Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

48 Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 12:48
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ku 'yan'uwana, kada yawancinku su zama masu koyarwa, domin kun sani, mu da muke koyarwa za a yi mana shari'a da ƙididdiga mafi tsanani.


Idan wani ya yi laifi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, laifi ya kama shi ko da bai sani ba. Alhakin laifin yana kansa.


Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu.


Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.


ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.


Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,


bisa ga bishara mai daraja ta Allah abar yabo, wadda aka danƙa mini.


Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’


Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi.


ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa'azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa,


Idan bisa ga kuskure wani mutum ya yi zunubi, sai ya ba da 'yar akuya bana ɗaya ta yin hadaya don zunubi.


idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi.


Sai Bitrus ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa na kowa da kowa ne?”


“Wuta ce na zo in zuba wa duniya. Sona fa? A ce ta huru!


[Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan ci kayan matan da mazansu sun mutu, kukan yi doguwar addu'a don ɓad da sawu. Saboda haka za a yi muku hukunci mafi tsanani.]


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ