35 “Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne.
35 “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci,
Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.
Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,
To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”
“Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.
Ko ɗaya ba wanda ya gaji, ba kuwa wanda ya yi tuntuɓe. Ba su yi gyangyaɗi ko barci ba. Ba abin ɗamarar da ya kwance, ba igiyar takalmin da ta tsinke.
Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.
don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,
Takan himmantu ta yi aiki tuƙuru.
Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.
Ku dai zama kamar mutane masu jiran ubangijinsu ya dawo daga gidan biki, da zarar ya ƙwanƙwasa su buɗe masa.