Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 12:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Ai, al'umman duniya suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, ku kuwa, Ubanku ya san kuna bukatarsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 12:30
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ai, al'ummai ma suna ta neman duk irin waɗannan abubuwa, Ubanku na Sama kuwa ya san kuna bukatarsu duka.


Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.


To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku sāke yin zama irin na al'ummai, masu azancin banza da wofi.


“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.


Haka ma, ba nufin Ubanku da yake cikin Sama ba ne ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya hallaka.”


ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.


Domin ba ku ne kuke magana ba, Ruhun Ubanku ne yake magana ta bakinku.


In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba?


Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”


“Ku yi hankali kada ibadarku ta zama ta ganin ido. Domin in kun yi haka, ba za ku sami sakamako wurin Ubanku da yake a Sama ba.


Ku ma kada ku damu a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada kuwa ku yi alhini.


Ku ƙwallafa rai ga al'amuran Mulkin Allah, sai a ƙara muku da waɗannan abubuwa kuma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ