Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 12:28 - Littafi Mai Tsarki

28 To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 12:28
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”


Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.


To, ga shi, Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Domin “Duk ɗan adam kamar ciyawa yake, Duk darajarsa kamar furen ciyawa take, Ciyawar takan bushe, furen yakan kaɗe,


Ya ce musu, “Ina bangaskiyarku?” Suka kuwa tsorata suka yi mamaki, suna ce wa juna, “Wa ke nan kuma, har iska da ruwa ma yake yi wa umarni, suna kuwa yi masa biyayya?”


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”


Da Yesu ya lura da haka sai ya ce, “Ya ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da juna a kan ba ku zo da gurasa ba?


Ya ce musu, “Don me kuka firgita haka, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?” Sa'an nan ya tashi, ya tsawata wa iskar da ruwan. Sai wurin duk ya yi tsit!


Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!” Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?” “Ka yi shela, cewa dukan 'yan adam kamar ciyawa suke, Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.


Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ