Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 11:51 - Littafi Mai Tsarki

51 wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

51 wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 11:51
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan Kayinu, ta wurin wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta wurin bangaskiyar nan tasa har ya zuwa yanzu yana magana.


Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.


kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne.


A watan takwas a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo, ya ce,


Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.


Za ka faɗa musu ka ce, wannan ita ce al'ummar da ba ta yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnta ba, ba ta karɓi horo ba. Gaskiya kuma ta ƙare sam, ba ta a bakinsu.


Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ