Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 11:50 - Littafi Mai Tsarki

50 don alhakin jinin dukan annabawa da aka zubar tun daga farkon duniya, a bi shi a kan mutanen wannan zamani,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

50 Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 11:50
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

saboda kuma marasa laifi waɗanda ya kashe, gama ya cika Urushalima da jinin marasa laifi, Ubangiji kuwa ba zai gafarta wa Manassa ba.


Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila, An kama sojojinta, An kuma kakkarya bakunansu, Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya, Zai yi sakayya sosai.


“Ku aske gashin kanku, ku zubar da shi. Ku yi makoki a filayen tuddai, gama Ubangiji ya ƙi 'yan zamanin nan, ya rabu da su saboda fushinsa.


Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.


Allah yana tunawa da waɗanda suke shan wuya, Ba ya mantawa da kukansu, Yana kuma hukunta waɗanda suke cutarsu.


Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.


Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ