Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu?
Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”
Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”