Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 10:21 - Littafi Mai Tsarki

21 A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 10:21
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko da bishararmu a rufe take, ai, ga waɗanda suke hanyar hallaka kaɗai take a rufe.


A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,


Ya ƙaddara mu mu zama 'ya'yansa ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga nufinsa na alheri,


Hakika, ina gaya muku, duk wanda bai yi na'am da Mulkin Allah kamar yadda ƙaramin yaro yake yi ba, ba zai shiga Mulkin ba har abada.”


Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, “ ‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.


Yara da jarirai suna raira shi, Ka gina kagara saboda magabtanka, Domin ka tsai da maƙiyanka da abokan gābanka.


In kuwa ta same shi, sai ta tara ƙawayenta da maƙwabta mata, ta ce musu, ‘Ku taya ni farin ciki, don na sami kuɗin nan da na yar.’


In kuwa ya same ta, sai ya saɓo ta a kafaɗa, yana farin ciki.


Ubangiji Allahnki yana tsakiyarki, Mayaƙi mai cin nasara ne. Zai yi murna, ya yi farin ciki da ke. Zai sabunta ki da ƙaunarsa. Zai kuma yi murna da ke ta wurin raira waƙa da ƙarfi.


Ubangiji ya ce, “Sama kursiyina ce, duniya kuwa matashin sawuna ce. Daga nan wane irin gida za ku iya ginawa domina, wane irin wuri ne kuma zan zauna?


Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.


Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”


Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.


Ubangiji zai ɗauke ki amaryarsa, Za ku yi murna tare, Kamar murnar amarya da ango.


Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne, Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.


Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ