18 Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.
18 Sai ya amsa ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya.
Ya Sarkin Babila, kai da kake tauraron asubahi mai haske, ka fāɗo daga sama. A dā ka ci al'ummai da yaƙi amma yanzu an fyaɗa ka ƙasa.
Mala'ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga wani tauraron da ya faɗa a kan duniya daga sama, aka ba shi mabuɗin ramin mahallaka.
a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.
Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.
Duk mai aikata zunubi, na Iblis ne, don tun farko Iblis mai aikata zunubi ne. Dalilin bayyanar Ɗan Allah shi ne domin yă rushe aikin Iblis.
Wato tun da yake 'ya'yan duk suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato iblis, ta wurin mutuwarsa,
Sai ya kama macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,
Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”