Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.
Ashe, wanda rashin kaciya al'adarsa ce, ga shi kuwa, yana bin Shari'ar daidai, ba sai yă kāshe ka ba, kai da kake da Shari'a a rubuce da kuma kaciya, amma kana keta Shari'ar?
Ubangiji ya ce, “Mutanen Taya sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe mutanen sun kai ƙasar Edom. Suka karya yarjejeniyar abuta wadda suka yi.
“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.