Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar.
Sa'an nan zan cika maganar rantsuwa da na rantse wa kakanninku, da na ce zan ba su ƙasa wadda take cike da albarka kamar yadda yake a yau.’ ” Irmiya ya ce, “Amin, amin, ya Ubangiji.”
Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.
Ubangiji Allah na Sama wanda ya ɗauke ni daga gidan mahaifina daga ƙasar haihuwata, wanda ya yi magana da ni ya kuma rantse mini, ‘Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa,’ shi zai aiki mala'ikansa a gabanka. Za ka kuwa auro wa ɗana mata daga can.