Da suka kasa yarda a junansu, kafin su watse sai Bulus ya yi musu magana ɗaya ya ce, “Ashe kuwa, Ruhu Mai Tsarki daidai ya faɗa, da ya yi wa kakanninku magana ta bakin Annabi Ishaya cewa,
An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.
Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.”
Ubangiji ya ce, “Kada ka ji tsoro, ya barana Yakubu, Kada kuma ka yi fargaba, ya Isra'ila, Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa rai a kwance, Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.
“Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci daga zuriyar Dawuda Wanda zai ci sarauta. Zai yi sarauta da hikima, Zai aikata abin da yake daidai a ƙasar.
Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”
Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.