Ubangiji ne Mai Cetona, Shi ne garkuwata mai ƙarfi. Allahna, shi ne yake kiyaye ni, Lafiya nake sa'ad da nake tare da shi, Yana kiyaye ni kamar garkuwa, Yana kāre ni, ya ba ni lafiya.
Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.”
Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce, “Ubangiji ya cika zuciyata da murna. Ina farin ciki da abin da ya yi. Ina yi wa maƙiyana dariya, Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.
“Wata rana zan sāke tayar da birnin Dawuda Tankar yadda akan ta da gidan da ya rushe. Zan gyara garunsa, in sāke mai da shi. Zan sāke gina shi in mai da shi kamar yadda yake tun dā.