“Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa.
Domin zai zama mai girma a wurin Ubangiji, Ba kuwa zai sha ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Za a cika shi da Ruhu Mai Tsarki Tun yana cikin uwa tasa.
Sa'an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba'in. Sa'ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba.
Sai Hananiya ya tafi, ya shiga gidan. Da ya ɗora masa hannu, ya ce, “Ya ɗan'uwana Shawulu, Ubangiji ne ya aiko ni, wato Yesu, wanda ya bayyana a gare ka a kan hanyar da ka biyo, domin ka sāke gani, a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”