60 amma uwa tasa ta ce, “A'a, Yahaya za a sa masa.”
60 amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”
Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.
ya kuma umarci annabi Natan ya raɗa wa yaron suna Yedideya, wato ƙaunataccen Ubangiji.
Bayan wannan na yi jima'i da matata annabiya. Ta ɗauki ciki, ta haifi ɗa namiji, Ubangiji ya ce mini, “Ka raɗa masa suna, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’
Sai ya nema a ba shi allo, sa'an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki.
amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.
Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan'uwanku mai suna haka.”