57 To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.
57 Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.
Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.
Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya, Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba. Zai cika dukan abin da ya alkawarta, Ya hurta, ya kuwa cika.
A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.
Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa'an nan ta koma gida.
Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.