Allah ya ce, “A'a, matarka Saratu ita ce za ta haifa maka ɗa, za ka raɗa masa suna Ishaku. A gare shi zan tsai da alkawarina madawwami, da kuma ga zuriyarsa a bayansa.
Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka,
Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”
Zuriyarka kuwa za su zama kamar turɓayar ƙasa, za su kuma bazu zuwa gabas da yamma, kudu da arewa. Ta wurinka da zuriyarka, iyalan duniya duka za su sami albarka.