Dukan itatuwan jeji za su sani, Ni Ubangiji nakan sa manyan itatuwa su zama ƙanana, In sa ƙanana kuma su zama manya, In sa ɗanyen itace ya bushe, In sa busasshen itace kuma ya zama ɗanye, Ni Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata.”
Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”
“Wata rana zan sāke tayar da birnin Dawuda Tankar yadda akan ta da gidan da ya rushe. Zan gyara garunsa, in sāke mai da shi. Zan sāke gina shi in mai da shi kamar yadda yake tun dā.
Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.