50 Daga zamanai ya zuwa wani zamani, Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.
50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani.
Amma nakan gwada madawwamiyar ƙaunata ga dubban tsararrakin da suke ƙaunata, masu kiyaye dokokina.
“Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.
Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa, Yakan ji kukansu, ya cece su.
Bari dukan waɗanda suke tsoronsa su ce, “Ƙaunarsa kuwa tabbatacciya ce.”
Kamar yadda nisan sararin sama yake bisa kan duniya, Haka kuma girman ƙaunarsa yake ga waɗanda suke tsoronsa.
Abin al'ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka! Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma, Yana da banmamaki. Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.
Zai sa wa dukan waɗanda suke tsoronsa albarka. Babba da yaro.
Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa, Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
Amma yana jin daɗin waɗanda suke tsoronsa, Yana jin daɗin waɗanda suke dogara da madawwamiyar ƙaunarsa.
Hakika a shirye yake yă ceci waɗanda suke girmama shi, Kasancewarsa a ƙasar, ceto ne ga ƙasar.
Domin fa shi da yake Mai Iko, Manyan al'amura ya yi mini, Sunansa labudda mai tsarki ne.
Amma su yi tsoron Ubangiji Allahnsu, shi kuwa zai cece su daga hannun dukan abokan gābansu.