Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Luka 1:49 - Littafi Mai Tsarki

49 Domin fa shi da yake Mai Iko, Manyan al'amura ya yi mini, Sunansa labudda mai tsarki ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Luka 1:49
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kawo wa jama'arsa ceto, Ya kuma yi musu madawwamin alkawari. Mai Tsarki ne shi, Maɗaukaki!


Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki, Mai Tsarki ne shi!


Ya Ubangiji, ba wani kamarka, Kai mai girma ne, Sunanka kuma yana da girma da iko.


Ɗaukaka tā tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu.


A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”


Ku yabi Ubangiji Allahnmu, Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki! Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!


“Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji, Babu wani mai kama da shi, Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.


“Ya Ubangiji, wane ne kamarka a cikin alloli? Wa yake kamarka a cikin ɗaukaka da tsarki? Mai banrazana cikin mafifitan ayyuka, mai aikata mu'ujizai.


Suna ta kiran junansu suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Mai Runduna Mai Tsarki ne! Ɗaukakarsa ta cika duniya.”


Amma Ubangiji kana tare da ni Kamar jarumi mai bantsoro, Don haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe, Ba za su rinjaye ni ba. Za su sha kunya ƙwarai, Gama ba za su yi nasara ba. Ba za a manta da su ba.


Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”


Ya kuwa yardar musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shiga aladun. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugungunto ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka halaka a ruwa.


Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra'ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.


Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!


Wane ne wannan da yake zuwa daga Bozara cikin Edom? Wane ne wannan da ya sha ado da jajayen kaya, yana tafe, ga shi kuwa ƙaƙƙarfa? Ubangiji ne, mai ikon yin ceto, yana zuwa ya yi sanarwar nasara.


Domin fa shi ya dubi ƙasƙancin baiwa tasa. Ga shi, jama'a ta dukan zamanai, Za su ce mini mai albarka ce nan gaba.


Daga zamanai ya zuwa wani zamani, Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ