A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.
Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’
Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”
Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Sa'an nan wani daga cikin zuriyar Dawuda zai zama sarki. Zai mallaki jama'a da aminci da ƙauna. Zai aikata abin da yake daidai da hanzari, zai sa a aikata adalci.
“Ga shi, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan tsiro da wani mai adalci daga zuriyar Dawuda Wanda zai ci sarauta. Zai yi sarauta da hikima, Zai aikata abin da yake daidai a ƙasar.
“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.
Ina umartar mutanen da suke cikin mulkina su yi rawar jiki, su ji tsoron Allah na Daniyel, “Gama shi Allah ne mai rai, Madawwami, Sarautarsa ba ta tuɓuwa, Mulkinsa kuma madawwami ne.