4 domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.
4 Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata.
wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu'a, duk sa'ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.
A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.
Tun da yake muna da sa zuciya irin wannan, to, muna magana ne gabanmu gaɗi ƙwarai.
Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.
Yanzu kuma ya Ubangiji, dubi wannan kashedin nasu, ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali,
Ku tafiyar da al'amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.