Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.
Waɗanda suka ragu cikin Isra'ila, Ba za su aikata mugunta ba, Ba kuma za su faɗi ƙarya ba, Gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba. Za su yi kiwo, su kwanta, Ba wanda zai tsorata su.”
Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.
Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.
Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”