An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.
Idan mutuwarku tare da Almasihu ta 'yanta ku daga al'adun duniyar nan, me ya sa kuke zama har yanzu kamar ku na duniya ne? Don me kuke bin dokokin da aka yi bisa ga umarnin 'yan adam da koyarwarsu,
Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.
In kuwa tun muna maƙiyan Allah aka sulhunta mu da shi ta mutuwar Ɗansa, to, da yake an sulhunta mu, ashe kuwa, za a fi kāre mu ta wurin rayuwarsa ke nan.
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.
A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.
Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”
Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.
Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.
Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.