21 Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa 'ya'yanku, domin kada su karai.
21 Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.
Ubangiji yana tsauta wa waɗanda yake ƙauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa ɗan da yake fāriya da shi.
Kamar yadda uba yake yi wa 'ya'yansa alheri, Haka nan kuwa Ubangiji yake yi wa masu tsoronsa alheri.
Domin kun san yadda muka yi wa kowannenku gargaɗi kamar uba da 'ya'yansa ne, muna ta'azantar da ku, muna kuma ƙarfafa muku umarnin, cewa
Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.