Haka kuma, ku maza, ku yi zaman ɗa'a da matanku, kuna girmama su, da yake su ne raunana, gama ku abokan tarayya ne na Allah. Ku yi haka don kada wani abu ya hana ku yin addu'a tare.
Ka yi nishaɗi da matar da kake ƙauna, dukan kwanakin ranka na banza waɗanda Allah ya ba ka a wannan duniya, ka more kowace rana, wannan ne kaɗai rabonka na wahalar aikinka a duniya.
Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta'azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
“Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.