18 Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.
18 Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.
Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.
Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne.
Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
Ban yarda mace ta koyar, ko kuma ta yi iko da maza ba, sai dai ta zama shiru.
Sa'ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya.”
Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce.
Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.
Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba.
domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.