Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.
Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”
Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.
Shi ne kuwa muke sanarwa, muna yi wa kowane mutum gargaɗi, muna kuma koya wa kowane mutum da matuƙar hikima, da nufin mu miƙa kowane mutum cikakke a cikin Almasihu.