Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Kolossiyawa 2:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Irin waɗannan dokoki kam, lalle suna da'awar hikima ta wajen yin ibadar da aka ƙago, ta wurin yin tawali'un ƙarya da kuma wahalar da jiki, amma ko ɗaya ba su da wata daraja ga sarrafar halin mutuntaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Kolossiyawa 2:23
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.


Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali'un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala'iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka,


Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.


Su ne masu hana aure da cin abinci iri iri, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka ba da gaskiya, suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya.


(Wato, ana nufin abubuwan da, in an ci su sukan ruɓa duka).


Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu yake yi wa Ikkilisiya,


Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ