Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Kolossiyawa 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Almasihu ya yi muku ce, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Kolossiyawa 2:11
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.


Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al'amuran ganin ido,


Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke a ciki, wanda yake lalacewa saboda sha'awoyinsa na yaudara,


Wato, mun sani an gicciye halayenmu na dā tare da shi, domin a hallakar da ikon nan namu mai zunnubi, kada mu ƙara bauta wa zunubi.


Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.


Ubangiji Allahnku kuma zai tausasa zuciyarku da ta 'ya'yanku domin ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da zuciya ɗaya da dukan ranku, domin ku rayu.


An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.


Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.


Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.


Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.


Amma Almasihu ya riga ya zo, yana babban firist na kyawawan abubuwan da suke akwai. Masujadar da yake hidima a ciki mafi ɗaukaka ce, mafi kammala kuwa (wadda ba yin mutum ba ce, wato, ba ta wannan halittacciyar duniya ba ce).


Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


Gama mun sani in an rushe jikinmu na wannan duniya, Allah ya tanadar mana jiki a Sama, wato, wanda shi kansa ya yi, wanda zai dawwama.


Allahn da ya halicci duniya da dukkan abin da yake cikinta, shi da yake Ubangijin sama da ƙasa, ba ya zama a haikalin ginin mutum.


Duk da haka Maɗaukaki ba ya zama a gidaje, ginin mutum. Yadda Annabi Ishaya ya ce,


Da rana ta takwas ta kewayo da za a yi masa kaciya, aka sa masa suna Yesu, wato sunan da mala'ika ya faɗa kafin ya zauna a ciki.


“Mun ji ya ce, wai zai rushe Haikalin nan da mutane suka gina, ya gina wani cikin kwana uku, ba kuwa ginin mutum ba.”


Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa?


Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ