Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Kolossiyawa 2:1 - Littafi Mai Tsarki

1 To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Kolossiyawa 2:1
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda wannan nake shan wahala, nake fama da matuƙar himma, wadda yake sa mini ta ƙarfin ikonsa.


kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.


tana cewa, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa ikilisiyoyin nan bakwai, wato ta Afisa, da ta Simirna, da ta Birgamas, da ta Tayatira, da ta Sardisu, da ta Filadalfiya, da kuma ta Lawudikiya.”


To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,


suna baƙin ciki tun ba ma saboda maganar da ya faɗa ba, cewa ba za su ƙara ganinsa ba. Daga nan suka rako shi har bakin jirgi.


Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,


Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.


Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!


To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.


Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]


Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.


Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.


Sai Rahila ta ce, “Da gawurtacciyar kokawa na yi kokawa da 'yar'uwata, har na yi rinjaye,” sai ta raɗa masa suna Naftali.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ