8 ya kuma sanasshe mu ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
8 wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
Amma ina roƙonku 'yan'uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunar nan da Ruhu yake bayarwa, ku taya ni yin addu'a da naciya ga Allah saboda kaina,
Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.
saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,
Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,
ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.
Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.
Ba abin da yake ɓoye, sai domin a bayyana shi a gaba. Ba kuma wani abin da yake asiri, sai domin a bayyana shi a gaba.