Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Kolossiyawa 1:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Saboda wannan nake shan wahala, nake fama da matuƙar himma, wadda yake sa mini ta ƙarfin ikonsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Kolossiyawa 1:29
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma saboda alherin Allah na zama yadda nake, alherin da ya yi mini kuwa ba a banza yake ba. Har ma na fi kowannensu aiki, ba kuwa ni ba, alherin Allah ne da yake zuciyata.


da kuma ko mene ne girman ikonsa marar misaltuwa da yake zartarwa a gare mu, mu masu ba da gaskiya, wato zartarwar ƙarfin ikon nan nasa,


An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.


Domin Allah shi ne mai aiki a zukatanku, ku nufi abin da yake kyakkyawan nufinsa, ku kuma aikata shi.


yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.


To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba.


ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku.


Ya ku 'yan'uwa, kuna iya tunawa da wahala da famar da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku, duk sa'ad da muke yi muku bisharar Allah.


Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.


kuna riƙe da maganar rai kankan, har a ranar bayyanar Almasihu in yi taƙama, cewa himmata da famana ba a banza suke ba.


Dukan waɗannan Ruhu ɗaya ne da yake iza su, yake kuma rarraba wa ko wannensu yadda ya nufa.


Har ya zama mini abin buri in sanar da bishara, a inda ba a taɓa sanar da sunan Almasihu ba, don kada in ɗora ginina a kan harsashin wani,


Na sani kana haƙuri, kana kuma jimiri saboda sunana, ba ka kuwa gaji ba.


Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.


kuna shan fama irin nawa wanda kuka gani, wanda kuke ji nake sha har yanzu.


Sai dai ku yi zaman da ya cancanci bisharar Almasihu, domin ko na zo na gan ku, ko kuwa ba na nan, in ji labarinku, cewa kun dage, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya, kuna fama tare saboda bangaskiyar da bishara take sawa,


Ɗaukaka tā tabbata ga wannan da yake da ikon aikatawa fiye da dukkan abin da za mu roƙa, ko za mu zata nesa, wato, aikatawa ta ƙarfin ikonsa da yake aiki a zuciyarmu.


In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.


In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri.


da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.


Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.


Akwai kuma aiki iri iri, amma Allah ɗaya yake iza kowa ga yin kowannensu.


Amma ina roƙonku 'yan'uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma ƙaunar nan da Ruhu yake bayarwa, ku taya ni yin addu'a da naciya ga Allah saboda kaina,


“Ku yi famar shiga ta ƙunƙuntar ƙofa. Don ina gaya muku, mutane da yawa za su nemi shiga, amma ba su iya ba.


Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba.


An kuma binne ku tare da shi a wajen baftisma, inda kuma aka tashe ku tare da shi saboda bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ