Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Kolossiyawa 1:25 - Littafi Mai Tsarki

25 wadda na zama mai hidimarta bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da Maganar Allah sosai,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Kolossiyawa 1:25
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

in dai kun ji labarin mai da ni mai hidimar alherin Allah wanda aka yi mini baiwa saboda ku,


Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.


In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau.


muka kuma aiki Timoti ɗan'uwanmu, bawan Allah kuma na al'amarin bisharar Almasihu, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku a kan al'amarin bangaskiyarku,


Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan.


To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?


An kuwa sa ni mai hidimar wannan bishara, a bisa ga baiwar alherin Allah da aka yi mini ta ƙarfin ikonsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ